Pauline Zerla
|

LPBI Takardar Bayani | Damuwa, Kiyaye Tashin Hankali da Samar da Haɗin Kai: Ɗaukar Darrusa Daga Labaran Matasa na Tashin Hankali a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Abstract

Takardar bayanan na gabatar da sakamakon bincike daga rahoton bincike na RESOLVE Network “Fargaba, Kiyaye Tashin Hankali da Samar da Haɗin Kai: Ɗaukag darrusa daga Labaran Matasa na Tashin Hankali a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya,” na Pauline Zerla. A cikin shekaru goma tun lokacin da aka samu sababbin tashe-tashen hankula a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (CAR), an yi ta samun matasa a cikin nau’ukan tashe-tashen hankula mabambanta waɗanda suka shafi tilasta shiga cikin tawagar mutane da ke ɗauke da makamai ba a ƙarƙashin gwamnati ba, da kuma shiga cikin lamuran ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai a karkara. Wannan bincike ya nazarci matakan sake samar da haɗin kai a matsayin wani matakin fahimtar yadda fargaba, kare faruwar tashin hankali, da kuma samar da zaman lafiya ke da alaƙa da juna.