Pauline Zerla
|

LPBI Takardar Bayani | Amfani da Hoton Bayanin Mutane a Matsayin Hanyar Gudanar da Bincike: Ɗaukar Darrusa Daga Bincike Game Da Tashin Hankali da Sake Samar da Haɗin Kai a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Abstract

Wannan takardar bayanin na abatar da dabarun gudanarwa domin dubawa waɗanda aka samo daga binciken da aka gudanar domin rahoton RESOLVE Network, “Fargaba, Tashin Hankali Kariya da Sake Samar da HaɗinKai: Ɗaukar darrusa daga Labaran Tashin Hankalin Matasa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya,” na Pauline Zerla. Ƙari a kan fitattun hanyoyin tattara bayanai kamar su hira da tsararriyar tattaunawa cikin tawaga, yayin tattara bayanan wannan rahoton an yi amfani da dabarar ɗaukar hotunan bayanai daga mutanen da suka tsinci kansu cikin damuwa. Amfani da hotunan bayanan mutane—hotunan da ke wakiltar rayuwar mutane tare da nuni ga abubuwan da suka fuskanta a rayuwa— a cikin bincike zai ba da dama ga mutane su yi tunani game da yanayin damuwa da zasu iya shiga ta tsarin mara magana. Lura da alamun dacewar wannan dabarar tattara bayanai a binciken da za a gudanar nan gaba dangane da tashe-tashen hankula da sake samar da haɗin kai da lamarin lafiyar ƙwaƙwalwa da fargaba, wannan takardar bayanin ta kawo taƙaitaccen bayani game da dabarun amfani da wannan tsari tare da fatan waɗansu ma za su ɗauki hannu domin yin amfani da ita a matsayin tasu.